Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kano: Gobara da hadura sun hallaka mutane da dama a watan da ya gabata

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce, mutane tara ne suka rasa rayukansu, sakamakon ibtila’in gobara da hadurran ababen hawa da suka wakana a watan Fabrairu da ya gabata.

A cewar hukumar, an buga mata kira ta wayar tarho har sau tamanin da biyar yayin da ta samu nasarar ceto mutane talatin da daya.

Jami’in yada labarai na hukumar, Sa’id Muhammed Ibrahim ne ya bayyana haka, yayin zantawar sa da tashar Freedom Rediyo da yammacin yau.

Sa’id Muhammed Ibrahim ya kuma ce an yi asarar naira miliyan ashirin da bakwai da dubu dari da talatin da hudu da dari biyu cikin wa’adin.

‘‘Mun kuma samu nasarar tseretar da dukiyoyin jama’a da adadin kudinsu ya kai naira miliyan dari uku da talatin da bakwai da dubu dari da hudu’’. A cewar sa.

Ya kara da cewa, hukumar ta samu nasarar ceto mutane arba’in wadanda suka fada ibtila’I daban-daban cikin wannan wa’adi na watan Fabrairu.

Haka zalika kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kanon ya ce, hukumar ta karbi kiraye-kiraye da bana gaskiya ba, har guda goma sha uku.

Karin labarai:

Gobara ta tashi a gidan dan majalisar wakalai na jihar Zamfara

Gobara ta tashi a kasuwar GSM ta Alfin a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!