Labarai
Tsaftar Muhalli- An rufe gidajen man Kurfi da Audu Manager
Gwamnatin jihar Kano ta rufe gidajen man Kurfi da na Audu Manager da ke kan titin unguwar Kurna.
An rufe gidajen man ne bisa laifin karya dokar tsaftar muhalli ta karshen wata.
Gidajen man dai an kama su da laifin budewa tare da ci gaba da kasuwancin su a daidai lokacin da dokar tsaftar muhalli ta hana gudanar da harkoki.
Yayin da yake bada umarnin rufe gidajen man kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bukaci shugabannin gidajen man suje ma’aikatar muhalli don karbar hukuncin da ya dace da su, sakamakon yadda ma’aikatan shari’a suke tsaka da yajin aiki wanda hakan ne ya hana a yanke musu hukunci nan take.
You must be logged in to post a comment Login