Labarai
Tsaftar muhalli: An yanke tarar Naira dubu 100 ga hukumomin tashar Mota ta Rijiyar Zaki
Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta yanke hukuncn tarar Naira dubu 100 ga hukumomin tashar Motar Rijiyar Zaki a Kano.
An yanke hukuncin ne sakamakon samunsu suna lodin fasinjoji adaidai lokacin da ake gudanar da tsaftar muhalli na ƙarshen wata.
Da yake yanke hukuncin mai Shari’a Auwal Yusuf ya ce “Dukkanin motar da aka kama a cikin tashar tayi lodi za ta biya tarar Naira dubu 10, su kuma hukumomin tashar za su biya Naira dubu 100″.
Haka kuma ya bada umarnin tafiya da wasu direbobin mota a tashar don faɗaɗa bincike.
Jim kaɗan bayan fitowa daga tashar Motar ne kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya yi Allah wadai da halin da ya tarar da tashar a safiyar wannan rana.
Ya kuma ce, ba za su zuba ido wasu tsirarun mutane su rushe yunƙurin gwamnati na inganta muhalli ba, a don haka a shirya suke su ɗauki hukunci a kansu.
Daga nan ne kwamishinan ya ƙaddamar da dashen bishiya a unguwar ta Rijiyar Zaki a wani mataki na inganta muhalli.
You must be logged in to post a comment Login