Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Tsaftar muhalli: Za mu ɗauki tsatstsauran mataki kan ƴan sahu -Nasiru Garo

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta fito da wasu tsauraran matakai akan matuƙa baburan daidaita sahu, sakamakon yadda suke karya dokar tsaftar muhalli.

Kwamishinan muhalli Nasir Sule Garo ne ya bayyana hakan, yayin duban tsaftar muhalli da aka gudanar yau akwaryar birnin Kano.

Ya ce, kwamitin duban tsaftar muhalli ya lura da yadda masu adaidaita sahu ke sintirin daukan fasinjoji a kan titin duk da cewa doka ta hana hakan a safiyar asabar din ƙarshen kowanne wata.

Ya kuma ce, wannan shi ne karo na farko da ya fuskanci irin wannan matsala daga wajen matuƙa baburan daidaita sahun, tun bayan kama aikinsa a ma’aikatar a don haka zai ɗau mataki a kai.a

Yayin duban tsaftar muhallin kwamitin ya zagaya sassa daban daban na ƙwaryar birnin Kano don ganin yadda aikin ke gudana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!