Kiwon Lafiya
Tsaftar muhalli: za mu hana yanka dabbobi a cikin unguwnni daga bana- Sarkin Tsaftar Kano
Sarkin tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmad Garzo ya ce, daga shekarar bana gwamnatin Kano za ta fito da wani tsari da zai hana yanka dabbobi a cikin unguwanni.
A cewar sa, yanka dabbobi a cikin unguwanni a lokacin bikin sallah babba, na haifar da cututtuka ga al’ummar da ke zaune a yankin.
“Za mu bai wa gwamnati shawarar cewa, ta hana yankan dabbobi a cikin unguwanni, tare da bata shawarar a rika tafiya mayanka aje can ayi aikin dabbar don kyautata muhalli” inji sarkin tsafta.
Sarkin tsaftar wanda shi ne mashawarcin gwamna kan harkokin muhalli ya ce, tuni suka dauki matakin baza dakarun tsaftar muhalli a sassa daban-daban don daukan mataki kan masu karya doka.
“Ba za mu lamunci masu yin babbakar kawuna da fata su rika kona taya don yin aikin a cikin unguwanni ba, don haka dakarun mu za su sanya iadanu sosai don hana masu aikata.
Alhaji Ja’afaru Ahmad Gwarzo ya ce, akwai kotun tafi-da-gidan ka kan tsaftar muhalli da za hukunta duk wanda aka kama da laifin.
You must be logged in to post a comment Login