Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Anyi wa dan wasan Ac Milan Castillejo Fashi a Italiya

Published

on

An yiwa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ac Milan dan kasar Andalus wato Spain, Samu Castillejo fashi a birnin Milan na kasar Italiya a yammacin jiya Talata.

Castillejo, wanda aka kaiwa hari ya yin fashin yana kan hanyar sa ta tafiya ne, wanda fitilar dakatar wa ta tsayar da hakan ya jawo akayi masa fashin Agogon hannu.

Mai shekaru 25, Castillejo ya bayyana hakan ne a shafin sa na Instagram,  in da ya tambaya  da cewar mai yake faruwa ne a Milan ? Mutum biyu sun tare ni da bindiga sun kwace mun Agogo na, sai dai in cikin koshin lafiya, nagode.

Labarai masu alaka.

Ronaldinho ya shaki iskar ‘yanci

Yanzu -yanzu an dage gasar wasanni ta kasa saboda barazanar Corona

Castillejo, da kungiyar sa ta Ac Milan, na shirin zuwa Turin, a wasan da kungiyar zata fafata zagaye na biyu da takwarar ta Juventus, a wasan kusa da na karshe na cin kofin kalubalen kasar Italiya,  wanda  za’ayi ranar Jumma’a.

A baya dai kungiyoyin biyu sun tashi wasan farko kunnen doki 1-1, a watan Fabarairun daya gabata a filin wasa na Sansiro dake birnin Milan.

Kungiyar ta Ac Milan, zata fafata wasan ta na farko a gasar kasar Italiya, in an dawo bayan  tsaikon Annobar Corona, ranar 22 ga watan Yuni, da takwarar ta Lecce.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!