Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga Corona cikin kwana bakwai.

Published

on

Mataimakin gwamnan Bauchi Baba Tela wanda aka tabbatar ya kamu da cutar Covid-19 a makon da ya gabata ya samu sauki, an kuma sallame shi daga asibiti.

Shugaban hukumar bunkasa lafiya a matakin farko na jihar Bauchi Dakta Rilwanu Muhammad  ne ya bayyana hakan ranar Laraba lokacin da yake gabatar da jawabi game da halin da ake ciki kan masu dauke da cutar a jihar.

Idan za a iya tunawa a ranar uku ga watan Yunin 2020 ne aka tabbatar da cewa mataimakin gwamnan na Bauchi ya kamu da cutar Covid-19.

Baba Tela wanda shine shugaban kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar Covid19 da cutar Lassa a jihar Bauchi an killace shi tare da mutanen da ya yi mu’amala da su.

Shugaban hukumar lafiyar a matakin farko na jihar Bauchi y ace an killace mataimakin gwamnan Bauchin har tsawon kwanaki tara kamar yadda gidan talibijin na kasa NTA ya wallafa a shafinsa na internet.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!