Labarai
Tsarikanmu ga masu shigo da kayyayaki ta ruwa na da alaka da manufofin shugaba Tunubu- NPA

Hukumar Kula da Tashohin jiragen ruwa ta Najeriya NPA, ta ce, tsarin da hukumar ke samarwa ga masu shigo da kayyayaki ta ruwa ya na da alaka da manufofin shugaban kasa bola Ahmad Tunubu.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Dantsho, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yin jawabi ga masu ruwa da tsaki na hukumar da kuma abokan huldarta.
Dantsoho, ya ce, ci gaban da hukumar ke samu a yanzu na da alaka da manufofin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke kokarin samarwa a harkokin da suka shafi bangaren sufuri a Najeriaya.
Haka kuma, ya kara da cewa, masu shigo da kayyakli ta ruwa sun samu sauki matuka, ta hanyar rashin samun jinkiri yayin fitar da kayyyaki, inda ya gode musu sakamakon goyan bayan da suke bayarwa ta hanyar cika ka’idojin da suka dace.
You must be logged in to post a comment Login