Ƙetare
Tsarin banki a Afghanistan na neman durkushewa
Tsarin banki a Afghanistan na neman durkushewa, kamar yadda wani shugaban ɗaya daga cikin manyan bankunan ƙasar ya bayyana.
Shugaban bankin Musulunci na Afghanistan, Syed Moosa Kaleem Al-Falahi ya ce kwastamominsu na cikin fargaba kuma sha’anin hada-hadar kuɗi na cikin wani hali.
Mista Al-Falahi ya ce a halin yanzu Taliban na neman agaji ne daga China da Rasha.
Tun bayan da Taliban ta karɓi mulkin Afghanistan a watan Agusta ne ƙasashen Yamma da dama suka tsuke bakin aljihunsu suka daina tura tallafin kuɗi cikin bankunan na Afghanistan.
You must be logged in to post a comment Login