Labarai
Tsarin yadda za a gabatar da muƙabalar Malaman Kano
Gwamnatin jihar Kano ta yi ƙarin haske kan shirinta na gabatar da Muƙabala tsakanin Malamai.
Gwamnatin dai ta sanya ranar Lahadi, bakwai ga watan Maris mai kamawa matsayin ranar da za a fafata a wannan muƙabalar.
Kwamishinan al’amuran addini na Kano Malam Muhammad Tahar Adamu Baba Impossible ya yiwa Freedom Radio ƙarin bayani a kai.
A cewar sa, mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku shi ne babban baƙo a yayin muhawarar.
Sauran waɗanda za su jagoranci zaman sun haɗa da, sakataren majalisar ƙoli ta addinin Musulunci Farfesa Shehu Galadanci da babban limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen.
Baba Impossible ya ƙara da cewa, zaman muƙabalar na ƙeƙe da ƙeƙe zai tattauna ne a kan wasu muhimman batutuwa guda tara.
Yanzu haka, tuni aka bai wa majalisar malamai ta jihar Kano damar zaƙulo zaƙaƙuran malaman da za su fafata da Malam Abduljabbar Kabara, daga dukkan ɓangarorin addini da ke Kano a cewar sa.
You must be logged in to post a comment Login