Connect with us

Kasuwanci

Tsarinmu na kawar da rashin ayyukan yi ya yi nisa- Gwanatin Kano

Published

on

Gwanatin jihar Kano, ta ce, tsarinta na kawar da rashin aikin yi a tsakanin matasa ya yi nisa, duba da cewa duk shekara ana yaye matasa sama da dubu daya a makarantar horasa da matasa sana’o’in dogaro da kai ta Aliko Dangote Skills Aquisition Center.
Shugaban makarantar Alhaji Alkasim Hussain Wudil, ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da freedom radiyo.

Ya ce, ana horas da matasan ne kan sana’o’i daban-dabam ta yadda za su iya yin gogayya da duk mai sana’ar hannu a fadin duniya.

Alhaji Alkasim Hussain Wudil, ya kara da cewa gwamantin jihar Kano ce ta ke samar da duk injina da sauran kayyayakin koyo da koyarwa a makarantar.

Da ya ke jawabi kan tsarin da ake bi na daukar dalibai a makarantar, Daratkan sashen horaswa Malam Abubakar, Yunusa cewa ya yi kowane dalibi na zuwane ta hanyar karamar hukumarsa.

Haka kuma, ya ce, Makarantar ta na horas da matasa a fanonin goma sha bakwai da kuma wasu fannonin da za a fara koyarwa nan ba da jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!