Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Ƴan bindiga sun sako matar ɗan kasuwar da suka yi garkuwa da ita a Kano

Published

on

Ƴan bindiga sun sako matar ɗan Kasuwa da ɗanta da suka yi garkuwa da su a Kano, bayan shafe kwanaki 39 a hannunsu.

Ɗan Kasuwar Alhaji Ishu Adam Mai Taki ya shaida wa Freedom Radio cewa, da yammacin Alhamis ne matar tasa da ɗansa suka dawo gida.

Ya ce, sun dawo cikin ƙoshin lafiya, sai dai bai yi ƙarin bayani kan yadda suka kuɓuta ba.

Tun a watan Disamba ne dai ƴan bindigar suka afka wa gidan ɗan kasuwar a garin Falgore na ƙaramar hukumar Rogo a Kano.

A nan ne suka yi awon gaba da matar, Hajiya Binta Isah da ɗanta mai shekaru huɗu.

Sannan suka ƙone motar jami’an sintiri ta ƙaramar hukumar Rogo.

Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da kuɓutar matar da ɗanta kamar yadda mai magana da yawun ta DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Freedom Radio.

Sai dai shima bai yi ƙarin bayani kan yadda suka kuɓuta ba.

Ku kasance da Freedom Radio cikin shirin An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safiyar Jumu’a domin jin ƙarin bayani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!