Connect with us

Labarai

Tsaro: Ƴan bindiga sun hallaka Manoma 8 a Zamfara

Published

on

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, wasu Mahara sun halaka mutane 8 a safiyar yau Asabar a ƙauyan Damaga da ke karamar hukumar Marudun ta jihar Zamfara.
Lamarin ya farune lokacin da al’ummar yankin suka fita aikin gona inda ƴan bindigar suka buɗe musu wuta kamar yadda wani ganau ya shaidawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaɓa.

Wakilin namu ya tuntiɓi jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar ta Zamfara SP. Shehu Muhammad inda ya ce, suna kan bincike amma ya bashi lokaci.
Sai dai har kawo lokacin hada wannan rahoto bamu samu ji daga gareshi ba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!