Connect with us

Labarai

Matar Marigayi Janar Attahiru na nan a raye

Published

on

Jaridar Leadership ta nemi afuwa kan rahoton da ta fitar na cewa hatsarin saman soji ya rutsa da matar Babban Hafsan Sojin ƙasar nan Hajiya Fati Attahiru.

A wata sanarwa da jaridar ta fitar ta ce, ta yi kuskure wajen wallafa labarin, sakamakon yaudarar ta da majiyoyin da ta aminta da su suka yi.

Jaridar ta ce, ta yi nadama kan faruwar lamarin, saboda haka ta nemi afuwar dangin marigayin da sauran jama’a da suka ci karo da labarin.

Bayan rahoton Leadership na farko dai an yi ta yaɗa rahoton cewa, hatsarin ya rutsa da ran mai ɗakin Janar Attahirun.

Sai dai rahotonni sun tabbatarwa da Freedom Radio cewa, matar marigayin tana nan da ranta kuma bata cikin tawagar da hatsarin ya rutsa da su.

Yanzu haka ma, tana birnin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!