Labarai
Tsaro: An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Jangeɓe
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar takaita zirga-zirgar jama’a na tsawon awanni ashirin da hudu a garin Jangebe da ke yankin karamar hukumar Talata Mafara, farawa daga jiya laraba uku ga watan Maris.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin da ya barke a garin na Jangebe kwana daya bayan sakin dalibai mata da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun harbi wani mazaunin garin na Jangebe sanadiyar tarzomar da ta tashi, wanda yanzu haka an kwantar da shi a asibiti don kula da lafiyarsa.
Bayanai sun ce tun farko al’ummar garin na Jangebe sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda gwamnatin jihar take gudanar da lamuran daliban da aka ceto su daga hannun ‘yan bindigar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar Sulaiman Tanau Anka, ta ce an dau matakin ne da nufin dakile yaduwar tarzomar.
‘‘Mun samu labaran sirri da ke cewa ‘yan bindiga suna amfani da kasuwar Jangebe wajen gudanar da harkokinsu, inda anan ne suke samun kayayyakin masarufi saboda haka muka yanke shawarar rufe kasuwar garin zuwa wani lokaci’’ a cewar kwamishinan yada labaran.
You must be logged in to post a comment Login