Labarai
Tsaro: Buhari yana ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tsaka da jagorantar taron majalisar kula da harkokin tsaro ta kasa a fadar Asorok da ke Abuja.
Taron shine irinsa na farko da shugaban kasar ya ke yi da sabbin manyan hafsoshin tsaro bayan nada su a watan Janairu.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Haka zalika sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministoci: Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ministan tsaro da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ministan kula da ‘yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi da kuma ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey onyeama.
A bangaren jami’an tsaro akwai: babban hafsan tsaron kasar nan Manjo Janar Lucky Irabor, babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, da takwaransa na sama Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amoo, da kuma babban hafsan sojin ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Haka kuma shima sufeto Janar na ‘yan sanda Muhammed Adamu da shugaban hukumar tsaron sirri ta DSS Yusuf Magaji Bichi da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA) Ambasada Ahmed Rufai da takwaransa na leken asiri na soji Manjo Janar Samuel Adedayo suna cikin mahalrta taron.
You must be logged in to post a comment Login