Kasuwanci
Tsaro: Buhari zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wata ganawa ta musamman da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken.
Rahotanni sun ce shugaba Buhari zai gana da mista Blinken ta kafar internet a gobe talata.
Wannan dai ita ce tattaunawa ta farko da mista Blinken zai yi da shugabannin nahiyar afurka tun bayan kama mulkin shugaba Joe Biden
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatan harkokin wajen Amurka Ned Price ya fitar, ta ce, yayin tattaunawa tsakanin sakataren harkokin wajen na Amurka da shugaba Buhari za a mai da hankali ta bangarorin kulla alaka kan mulkin dimukuradiya, tsaro da kuma tattalin arziki.
Haka zalika sanarwar ta kuma ce sakataren harkokin wajen na Amurka zai kuma gana da shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya bayan ganawa da shugaba Buhari da ministan harkokin wajen kasar nan Geoffrey Onyeama.
You must be logged in to post a comment Login