Labarai
Tsaro: dubunnan mutane na fuskantar barazanar yunwa a Nijar
Sama da mutane dubu 600 ne, ke fuskantar barazanar fadawa cikin matsalar karancin abinci a jihar Tillaberi dake yammacin jamhuriyyar Nijar.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kai tallafin jin kai OCHA reshen ƙasar ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Rahoton ya bayyana cewa yawan samun hare-haren ƴan bindiga kan manoma ne ya sanya yunwa musamman a yankin Anzourmawa
Magajin garin ƙaramar hukumar Sare kwara, Malam Hadi Djibo ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa, a baya bayannan ƴan bindiga sun kashe mutane uku a gonakin su.
Hukumar ta OCHA ta kuma bayyana cewa, bayaga barazanar rashin tsaro, janyewar ruwan sama da wuri a yankin Tilleberi ya sanya ƙarin samun ƙarancin abinci
You must be logged in to post a comment Login