Labarai
Tsaro – Gwamnatin jihar Niger ta rufe dukkan makarantun sakandaren Jihar
Gwamnatin Jihar Niger ta sanar da rufe makarantun sakandaren Jihar na tsawon makonni biyu, domin baiwa jami’an tsaro damar nazartar halin da ake ciki na kalubalen tsaro, inda aka rinka sace daliban makarantun kwana a wasu Jihohin arewacin Najeriya.
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Hajiya Hannatu Jibrin Salihu, ta ce za a rufe makarantun daga juma’ar nan 12 ga watan Maris, har zuwa ranar 26 ga Maris din na shekarar 2021.
“Bayan kammala nazartar yanayin tsaron da ake ciki a halin yanzu, za mu samu damar nakaltar hanyoyin domin baiwa al’umma tabbacin tsaron lafiyar ‘ya’yansu, da ta malamai da sauransu” in ji Kwamishiniyar.
“da ma can kuma gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello ya ba da umarnin rufe makarantun kwana 11 da na jeka-ka-dawo 11 sakamakon fuskantar klubalen tsaro” a cewar Hannatu Jibrin.
Tun bayan sace daliban makarantar Kagara ne gwamna Bello ya bayar umarnin gaggawa na rufe dukkan makarantun kwana da ke kananan hukumomi hudu na Jihar, da suka hadar da Rafi Munya Mariga da kuma Shiroro.
You must be logged in to post a comment Login