Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Masu cewa a kamani ba su san ciwon kansu ba – Sheikh Gumi

Published

on

Fitaccen malamin addinin Islaman nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya soki wadanda ke kiraye-kirayen cewa a kama shi sakamakon ganawa da ya ke yi da ‘yan bindiga.

Shehin malamin ya bayyana masu kiraye-kirayen da cewa ba su san ciwon kansu ba, yana mai cewa, taron da ya yi da ‘yan bindigar, jami’an gwamnati ma sun halarta.

A yayin zantawa da jaridar Daily Post, Sheikh Gumi ya ce ba shi ne mutum na farko da ya fara ganawa da ‘yan bindiga ba a kasar nan.

‘‘Ko da gwamnan jihar Kaduna ya gana da su shi ma takwaransa na jihar Zamfara ya gana da su, saboda haka me ya sa sai nawa ne zai zama abin magana?’’ a cewar Shehin Malamin.

‘‘Ni ba nine mutum na farko da na zanta da ‘yan bindiga ba. Kawai dai na bi sahun abin da wasu su ka yi ne, a matsayi na daya daga cikin malaman addini’’ inji Sheikh Gumi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!