Labarai
Tsaro: Jin haushin kin tattaunawa da ‘yan ta’adda ke kara tunzura su a Kaduna – El’Rufa’I
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babban abin da yasa ‘yan ta’adda suke yawan kai hare-haren ta’addanci a jihar shine rashin basu damar tattaunawa da gwamnati.
Gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, ne ya bayyana haka yayin da ake tattaunawa da shi a gidan Talabaijin na Channels.
El-rufa’i ya ce gwamnati ba za ta sauka daga kudirinta ba na kin tattaunawa da ‘yan ta’addah, yana mai cewa ba wayewa ba ce gwamnatin ta tattauna da masu laifi.
Ya ce abin da ya kamata gwamnatin tayi wajen magance ayyukan fashi da makami da kuma satar mutane ita ce daukar matakin da ya kamata ga mutanen dake aikata laifi.
You must be logged in to post a comment Login