Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Ƴan sanda sun yi holin ɓata gari 156 a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi holin mutane 156 da take zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Mutanen an kama su da makamai masu yawa da su ke ta’addanci da su.

Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya sanar da hakan, yayin taron manema labarai a shelkwatar ƴan sadan da ke Bompai.

Sama’ila Dikko ya ce laifukan da ake zargin su da aikatawa sun haɗar da fashi da makami da garkuwa da mutane da satar shanu, sai satar motoci da ayyukan daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma damfara.

Dikko ya ce, a tare da su an kwato bindigogi 10 da motoci 16 da adaidaita sahu 16 sai babura 3 da shanu da kwayoyin maye da wiwi wadda kuɗinta ya haura naira miliyan biyu.

Kwamishinan ya ce sun samu nasarar cafke ɓata-garin ne tun daga ranar 17 ga watan Yulin zuwa yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!