Labarai
Tsaunin Hayli Gubbi na Habasha ya yi aman Wuta

Wani tsauni a yankin arewa maso gabashin Habasha ya yi aman wuta a karo na farko cikin fiye shekara dubu goma sha biyu.
Tsaunin na Hayli Gubbi, ya fitar da talgen wutar inda hayaƙi ya turnuke sararin samaniya da nisan tafiyar kilomita goma sha huɗu.
Aman wutar ya haddasa fitar toka mai tsanani da ta mamaye yankunan.
Cibiyar da ke lura tsaunuka masu aman wuta ta ƙasar ya ce toka da tarkacen da aman wutar ya haifar ta mamaye wasu sassan sararin samaniyar ƙasashen Yemen da Indiya da Oman da kuma arewacin Pakistan.
Kawo yanzu dai abu wani rahoto game da adadin mutanen da suka jikkata sakamakon aman wutar.
You must be logged in to post a comment Login