Labarai
Tsoffin dalibai su rika tallafawa makarantunsu – Sarkin Kano
Daga Safarau Tijjani Adam
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce dole ne sai tsoffin dalibai sun taimakawa bangaren ilimi a kasar nan, la’akari da yadda gwamnatin kadai bazata wadatar ba.
Sarkin na Kano na bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron bikin cika shekara 30 na tsoffin daliban makarantar ‘yan mata ta Sumaila SOGA aji na 1990.
Sarkin wanda Fagacin Kano Alhaji Habibu Bello Dankadai ya wakilta, ya bukaci tsoffin daliban na Sumaila da su rika taimakawa makarantar tasu ta fannin ci gabanta don tabbatar da samun ilimi mai nagarta ga daliban yanzu.
Shugabar kungiyar Hajiya Halima Ibrahim ta ce, da ma kudirin kungiyarsu shi ne su tallafawa makarantar ta dora su a tafarkin da suke kai a yanzu.
Tana mai cewa, tuni suka fara tallafawa makarantar da gyaran wasu sassanta da kuma kayan koyo da koyarwa.
You must be logged in to post a comment Login