Labarai
Tsoffin Kansilolin APC da suka koma NNPP sun barranta kansu da kalaman Abdullahi Abbas

Shugaban kungiyar tsofaffin Kansilolin Jam’iyyar APC wanda wasun su suka sauya sheka zuwa NNPP sun, musanta maganar da shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya yi na cewar sun turo su ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusif, ne domin su yi musu yakin sunkuru na siyasa.
Shugaban kungiyar Sunusi Kata Madobi ne ya bayyana hakan yayin wani tattaki na musamman da suka gudanar kan nuna takaicin su da kalaman shugaban jam’iyyar ta APC.
Ya kuma ce, za su saka wa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Alkhairi bisa halarcin da ya yi musu.
Wasu daga cikin tsofaffun kansilolin da suka halarci taron sun bayyana mubaya’ar su ga gwamnan na Kano.
Sama da tsofaffun Kansilolin Jam’iyyar ta APC dubu uku ne dai suka yi tattaki dauke da Kwalaye da rubuntun barranta kansu da kalaman Shugaban jamiyyar ta APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas.
You must be logged in to post a comment Login