Kiwon Lafiya
Tsoffin yan PDP da suka koma APC sun musanta mikawa gwamnati bukatar dakatar da shari’ar Bukola Saraki
Kungiyar tsoffin ‘yan jam’iyyar PDP da suka koma APC, ta musanta mikawa gwamnati bukatar dakatar da shari’ar da ake yi wa shugaban majalisar dattijan kasar Sanata Bukola Saraki akan kin bayyana wasu kadarorin sa.
Shugaban kungiyar ta tsaffin ‘yan PDP da ke APC Alhaji Abubakar Baraje ne ya musanta rahoton, wanda ya bayyana shi a matsayin kage.
A nasa bangaren da yake musanta rahoton na baya bayan nan, kakakin kungiyar Muhammad Isa, ya ce dukkanin sharuddan da kungiyar tsaffin ‘yan PDP da ke APC suka mikawa gwamnati, bukatu ne na jam’iyya da basu shafi mutum guda ba.
Rahotanni dai na nuni da cewa daga cikin manyan bukatun da kungiyar ta tsaffin ‘yan PDP da ke cikin APC suka mikawa gwamnatin tarayya a taron su na ranar Litinin, akwai daukar mataki akan maida magoya bayan kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso saniyar ware a tarukan jam’iyyar APC da ya gudana a kananan hukumomin Bauchi da Kano.
Sauran bukatun sun hada da neman, a daina yi wa wasu ‘yan tsaffin jami’yyar PDPn bita da kulli, da sunan binciken hukumar EFCC mai yakar cin hanci da rashawa a Najeriya, da kuma dakatar da shari’ar shugaban majalisar dattijai kan kin bayyana wasu kadarorinsa da kotu ke sauraro.