Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar Dokoki ta sake sahale wa Abba Gida-gida nada mutane 20 mukamin SA

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince wa gwamna Engr Abba Kabir Yusuf, ya naɗa ƙarin mutane 25 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Majalisar ta amince ne bayan da shugabanta Jibril Isma’il Falgore, ya karanta wasiƙar buƙatar hakan da gwamnan ya aike mata.

Ta cikin wasiƙar, gwamnan, ya ce, zai naɗa mutanen ne domin ƙara samun damar gudanar da gwamnatinsa yadda ya kamata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa majalisar ta kuma gudanar da addu’a ta musamman ga tsohon shugaban shugaban majalisar marigayi Alhaji Yusuf Abdullahi Falgore, da ya rasu jiya Lahadi, tare da yin addu’a ga wasu fitattun mutane da suka rasu a nan Kano ciki har da tsohon dan majalisar da ya taba wakiltar Karamar hukumar Dala.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!