Labaran Wasanni
Magoya bayan Kano Pillars na kira da a kori mai horar da ‘yan wasan kungiyar
Dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sun nuna rashin jin dadin su bisa rashin nasarar da kungiyar ke ci gaba da yi a ‘yan kwanakin nan a gasar Firimiya ta kasa ta kakar wasanni ta bana.
Hakan dai na zuwa ne daidai lokacin da Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Star a wasan mako na hudu na gasar Firimiyar Najeriya.
Jigawa Golden Star dai ta doke Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a wasan da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Wannan rashin nasara ce ta kara harzuka magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars a filin wasan, inda suka dinga rera wakokin a sallami mai horar da ‘yan wasan kungiyar Ibrahim Musa Jigunu.
Da yake zantawa da manema labarai, Ibrahim Musa Jugunu, ya ce kungiyar ta rasa wasu kwararrun ‘yan wasa wanda har kawo yanzu ba a maye gurbin su ba, wanda hakan ke kara kawo wa kungiyar koma baya.
Ibrahim Musa ya kuma yi kira ga magoya bayan kungiyar su kwantar da hankalin su, nan ba da dadewa ba za’a samu gyara a kungiyar.
Kano Pillars dai ta yi rashin nasara wasanni biyu ne cikin wasanni uku da ta buga a kakar wasanni ta bana.
Wannan shine karo na farko da kungiyar ta kasa zura kwallo a wasanni uku a jere a gasar Firimiya ta kasa.
Tuni dai hukumar gudanawar kungiyar ta bawa mai horarwa Jugunu wa’adin samun nasara a wasanni uku ko kuma ta dau mataki.