Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Twitter bai dakatar da shafina ba – Lai Mohammed

Published

on

Ministan yaɗa labarai da al’adu na ƙasa, Lai Mohammed ya musanta labarin cewa dandalin Twitter ya dakatar da shafinsa.

A zantawarsa da jaridar Independent a ranar Talata, ministan ya ce, ba shi da wani shafi na karan kansa a Twitter.

Ministan ya ce, duk al’amuransa ana sanya su ne ta shafin ma’aikatar sadarwa na ƙasa wato @FMICNigeria.

Ya ci gaba da cewa “Duk da an buɗe shafuka da yawa a Twitter da suna na, amma ba nawa ba ne, ban ma taɓa buɗe shafin Twitter ba”.

A baya-bayan nan ne aka riƙa yaɗa rahoton cewa, dandalin sada zumunta na Twitter ya dakatar da shafin ministan.

Labarai masu alaka:

Takaddama : Majalisa ta kalubalanci Lai Muhammed kan ayyukan ma’aikatar sa

Babbar kotun jahar Rivers ta umarci Lai Muhammad kada ya sake buga sunan Uche Secondus cikin wadanda suka barnata dukiyar kasa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!