Labarai
UNICEF ta bada tallafin naira miliyan 105 ga makarantu Islamiyya
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya ya bada tallafin naira miliyan 105 domin tallafawa makarantun Ismaliyoyi da ke kananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano, domin taimakawa karatunsu na Islamiya.
Shugabar da take jagorantar Asusun tallafawa yara na UNICEF Mrs Miki Koide ce ta bayyana haka a yayin da ake bikin kaddamar da tallafawa karatun Kur’ani da makaratun Islamiyoyi a jiya a fadar gwamnatin jihar Kano.
Mrs Koide ta ce hukumar ta UNICEF zata ba da gudunmuwarta domin tallafawa makaratun Alkur’ani da kimanin naira miliyan 180 a wani shiri na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da Asusun Tallafawa kananan Yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF
Haka zalika shima gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada tallafin naira miliyan 10 da kayayyakin abinci ga alarammomin makaratun islamiya su dubu daya da aka dauko su daga tsangayu a fadin jihar Kano.
Gwamna ya kara da cewa tallafin nasa ya zama wajibi domin a cewarsa bada abinci a makaratu a fadin jihar Kano wajibi ne kamar yadda ake baiwa sauran tsarin makarantu na bai daya.
Ya ce gwamnatinsa ta fara sanya manhajja tsangaya a tsarin makarantun boko da ake da su a yanzu.