Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Wata mace ta kona kanta saboda tsananin kishi a Kano

Published

on

Wata Mata ta kona kanta saboda tsananin kishin an yi Mata kishiya a unguwar Gayawa dake karamar hukumar Ungogo a nan Kano.

Matar wace ake zargi da cewar sai da ta tanadi kayayyakin da zata konak anta kafin ta aikata hakan.

Matar mai suna Rabi ta kana kanta ne kasancewqar mijin ta mai suna Badamasi ya yi mata kishiya a kwanakin baya.

A yayin zantawa da wakilin mu Nasaru Salisu Zango wasu daga cikin  ‘yar uwar Rabi ake kiran ta da Mariya ta nuna bakin cikin ta kan afukuwar al’amarin tana cewar matar da ta kashe kanta kan kishi

Kazaliaka wani dan Uwan Mijin Badamasi da shi ma ake kiran Salisu Safiyanu  ya bayyana yadda almarin ya afku,  yana mai cewar  lokacin da ya shiga gidan  da yaga gawar Rabin a kone jikin sa ya dauki rawa.

Mace ta zubawa dan kishiyarta ruwan zafi a Kano

Bashi ya sanya wata mace kamuwa da ciwon zuciya a gidan Kurkuku

Har ila yau ita ma wata shakiyar Marigayiya Rabi  da ake kira da Ramatu  ta nuna bakin cikin ta kan matakin da Rabin ta dauka duk da cewar jami’an tsaro sun hana ganin gawar.

Da ya tutubi jami’an kashe gobara wakilin mu Abba Isa ya rawaito cewar, kakkakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’idu Muhammad Ibrahim ya ce yana bin didigin al’amarin don jin wane sashi ne na jami’an su

Haka kuma da ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sand ana jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa wakilin na mu Abba Isa ya tabbtar da afkuwar al’amarin yana mai cewa ofishin jami’an ‘yan sand ana kwana Uku sun dauki gawar Rabi don kai wa asibiti don tabbatar da tana raye ko ta mutu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!