Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Uwargida ta haifi ‘yan hudu a Jigawa

Published

on

Wata mata mai suna Sa’ade Abdullahi mai shekaru 30 a duniya ta haifi santala-santalan ‘ya’ya har guda 4 a lokaci guda.

Sa’ade Abdullahi da maigidanta Abdullahi Sulaiman sun fito ne daga kauyen Kantoga dake yankin karamar hukumar Birnin Kudu a jihar jigawa.

Sa’ade ta haihu ne a ranar talata 5 ga watan mayun shekara ta 2020, inda ta sunbulo ‘ya’ya hudu rigis, mata biyu, maza biyu, a karamin asibitin cikin garin Birnin Kudu.

Wannan iyali dai basu taba samun koda ‘yan biyu ba, sai a wannan haihuwa ta biyar da Allah ya kaddara musu samun ‘ya’ya hudu a lokaci guda.

Wakilin Freedom Radio Dutse Shamsuddin Abdullahi Limawa ya rawaito mana cewa har yanzu wannan mai jego tana kwance a asibiti, inda ta ke ci gaba da karbar kulawa, sakamakon rashin cikyakkiyar lafiya da karancin jini kari da rashin isash-shen nonan da jariran za su sha.

Mai gidan Sa’ade Abdullahi Sulaiman ya tabbatarwa da Freedom Radio Dutse cewa daya daga cikin tagwayen mata ta rasu kwanaki 2 bayan haihuwarsu.

Karin labarai:

Rashin tsaftace baki na kawo bari ga mata masu juna biyu

Daga zuwa zance Bazawara ta samu juna biyu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!