Kiwon Lafiya
WACP na gudanar da taronta na shekara-shekara karo na 49 a Kano

Ƙungiyar babbar Kwalejin koyar da Kwararrun likitoci ta yammacin Afrika, West African College of Physicians, ta na gudanar da babbana taronta na shekara-shekara na bana karo na 49 mai taken AGSM Kano 2025.
A ganawarsa da manema labarai dangane da taron, shugaban kungiyar na Najeriya Dakta Benjamin Uzo Chukwu, ya ce, subna shirya taron ne domin zama a gana tsakanin mambobin kungiyar wajen fito da sababbin hanyoyin magance cutuka a tsakanin mutane.
Haka kuma, ya ce, “Muna zagayawa domin gudanar da taron wayar da kan jama’a da kuma, duba marasa lafiya tare da basu magunguna a kyauta.”
“A wannan lokaci da muke gudanar wannan taro, mun ziyarci garin Bichi inda muka duba mutane marasa lafiya tare da basu kyautar magunguna, mun samu wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi har fiye da mutane 10,000, a cewarsa”
Haka kuma shugaban, ya bayyana motsa jiki da daina tu’ammali da Barasa da kuma Taba Sigari a matsayin manyan hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar da Daji.
Dakta Benjamin Uzo Chukwu, ya kuma bayyana bukatar gwamnatin tarayya da ta samasr da tsaro da kayan aiki da kuma inganta albashin ma’aikata domin magance matsalar tsallakewar jami’an lafiya zuwa kasashen waje, inda ya ce mafi yawan masu ficewa daga kasar nan suna tafiya ketare domin yin aiki suna yin haka ne domin nema wa kansu mafita, amma idan gwamanti ta yi abinda ya dace za a magance matsalar.
A nasa bangaren, Shugaban tsare-tsare da yaɗa labarai na ƙungiyar Farfesa Isah Abubakar, ya shawarci mutane da su tabbatar da cewa su na bin dokoki da kuma shawarwarin da likitocin ke ba su domin kula da lafiya yadda ya dace tare da kare kansu daga kamuwa da cutuka masu hatsari.
Haka kuma Farfesa Isah Abubakar, ya ƙara da cewa, za su ci gaba da gudanar da faɗakarwa da bada tallafin kiwon lafiya kyauta a nan Kano har zuwa ranar da za su kammala taron nasu na bana.
You must be logged in to post a comment Login