Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

WAEC : Ko ɗaliban Kano za su sami nasara a jarrabawar

Published

on

Tun da fari dai gwamnatin kasar nan ta sanar da ranar bude makarantun sakandire bayan da wasu jihohi suka yi barazanar buɗe makarantu a jihohin su domin rubuta jarrabawar WAEC.

Karamin ministan ilimi Mr. Chukwuemeka Nwajiuba shi ne ya bayyana hakan ya yin zaman kwamitin kartakwana kan yaƙi da cutar Korona na fadar shugaban ƙasa bayan da aka cimma yarjejeniya kan bude makarantu a faɗin ƙasar nan.

Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa hukumar shirya jarrabawar ta Afrika ta yamma Wato WEAC su amince a fara jarrabawar kamar yadda aka tsara a ranar 17 ga watan Augusta, ya yin da aka shirya tare da tsara lokacin da za a gudanar da sauran jarrabawa.

Tun bayan bullar annobar Korona aka rufe ilahirin makarantun ƙasar nan saboda gudun bazuwar cutar.

Kasancewar an yi ta samun kiki-kaka kan buɗe makarantun tsakanin hukumomi da masu ruwa da tsaki kan buɗe makarantun, wanda sai a makwanni biyu da suka gabata ne aka kai ha cimma matsaya.

Bayan samun sanarwa daban-daban masu cin karo da juna daga bakin ministan ilimi Malam Adamu Adamu da kuma ƙaramin minista Mr Chukwuemeka Nwajiuba kan buɗe makarantun.

A yau Litinin 17 ga wannan watan na Agusta ne, gwamnatin tarayya ta sanya don fara jarrabawar ta WAEC.

Al’umma da kuma masana a harkokin ilimi na ganin cewar lokacin da aka sanyawa ɗalibai ya matuƙar yin kaɗan.

Kazalika wasu na cewar, da dama daga cikin ɗaliban sun manta da karantu, wannan ne ya sanya wasu ke ganin cewar da wahala ɗaliban su ci wannan jarrabawar.

Karanta rahoton wakilin mu Abuhuraira Mukthar kan wannan batu:

A yau ne dalibai ‘yan ajin karshe na makarantun sakandire a fadin kasar nan suka fara rubuta jarrabawar kammala sakandire ta yammcin Afirka WAEC, kamar yadda gwamnatin tarraya ta bada umarni, bayan shafe tsawon watanni a gida sakamakon cutar korona.

A zagayen gani da ido da Freedom Radio ta yi a wasu daga cikin makarantun gwamnatin jihar Kano, ta gano yadda mafi yawa daga cikin makarantun suka yi biyayya ga dokokin da gwamnatin jihar ta shimfida don kare kai daga cutar Corona.

Haka kuma Freedom Radio ta gano yadda aka samu jinkiri wajen ƙarasowar kayayyakin rubuta jarabawar a wasu daga cikin makarantun.

Wasu dalibai da Freedom ta zanta da su, jim kaɗan bayan fitowar su daga jarrabawar sun bayyana cewa, jarrabawar ta gudana yadda ya kamata sai dai sun koka kan yadda jarrabawar ta zo musu a ƙurarren lokaci ta yadda basu samu damar yin isasshen karatu a gida ba.

Malama Umma Abdulkadir ita ce shugabar makarantar ‘yan mata ta GGAC goron Dutse, ta ce kasancewar a yau aka fara jarrabawar ya sanya suka fuskanci ƙalubale na rashin karasowar kayan jarrabawar akan lokaci, inda ta ce za suyi ƙoƙarin ganin sun magance matsalar a nan gaba.

Ta kuma ce, jarrabawar ta yau ta gudana yadda ya kamata bisa tsarin daukan matakan kariya daga cutar corona, sai dai ta buƙaci ɗalibai da su kara himma wajen fuskantar jarrabawarsu ta gaba.

A bana dai ana sa ran sama da dalibai miliyan daya da dubu dari biyar ne za su rubuta jarabawar a kasashen Ghana da Sierra Leone da Gambia da Liberia da kuma Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!