Labarai
Wajibi ne a fadada nasarar da aka samu a yaki da ‘yan ta’adda- shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne a fadada nasarar da aka samu wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin Najeriya zuwa sauran sassan kasar.
Muhammadu Buhari ya ce ‘yan ta’adda sun yi amfani da damar da su ka samu wajen mai da hankali da jami’an tsaron su ka yi wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas wajen cin karar su ba babbaka a sauran yankunan.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da Shugabannin kungiyar likitocin ta kasar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Dr. Francis Adedayo Faduyile wanda suka kai masa ziyara fadar Asorok a jiya Talata.
A cewar shugaba Buhari, a kullu yaumin harkar tsaro shine babbar lamari da gwamnatin sa ta sanya gaba, a don haka ya kara jaddada cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da daukar tsastsauran matakai wajen ganin an kawadda ayyukan batagari daga kasar nan.
Shugaban kasar ya kuma shaidawa kungiyar likitocin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bada fifiko ga bangaren lafiya da ilimi domin bunkasa tattalin arzikin kasar nan, sannan ya bukaci gwamnatin jihohi da kananan hukumomi da su tashi tsaye wajen ba da nasu gudunmowar wajen bunkasa bangarorin biyu.
Da ya ke gabatar da jawabi shugaban kungiyar likitoci ta kasa Dr. Francis Adedayo Faduyile, ya bukaci gwamnati da ta mayar da shirin Inshorar lafiya ya zamo dukkannin al’ummar kasar nan ne za su amfani da shirin.