Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu- yanzu : Shugaba Buhari na ganawar sirri da Buratai

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawar sirri da babban hafsan sojan kasar nan Tukur Buratai fadar sa dake Abuja.

Sai dai kawo yanzu ba’a bayyana dalilan ganawar sirrin ba da shugaban kasa yake da babban hafsan sojan kasar nan ba, amma rahotanin sun bayyana cewar ganawar ba zata rasa nasaba yaki da ‘yan ta’adda da sojojin kasar nan ke yi a yankin Arewa maso gabashin kasar nan ba.

A dai kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da manyan hafsoshin kasar nan a Abuja ya yin da ya gargadi su wajen sake yin dammar a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Ka zalika a yayin ganawar ya nuna bacin ran sa kan yadda ake samun rashin hadin kai a tsakanin sojojin kasar yana mai yin kira a gare su da kara kaimi wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Rubutu masu alaka : 

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro

An janye wa Magu jami’an tsaron da ke bashi kariya

Tukur Buratai:jajircewar a faggen daga da sadakarwa sojojin ya kawo cigaban tsaro a Najeriya

A dai ranar Asabar ne ‘yan bindiga suka kashe sojoji 16 da raunata 30 bayan da suka yi musu kwantan-bauna a yankin Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!