Labarai
Wakilan Kasashen 70 za su aikin magance kwararar baki
Wakilan wasu kasashen duniya 70 sun amince su yi aiki tare don magance matsalar kwararar baki a kasashe da dama, matakin da ke nuna goyan bayan shirin Majalisar Dinkin Duniya wanda wasu kasashe suka janye daga ciki.
Yayin da duniya ke fama da matsalar baki Yan gudun hijira sama da miliyan 21, daukacin kasashe 193 na Majalisar Dinkin Duniya banda Amurka, sun amince da wani daftari a watan Yuli da zai taimaka wajen dakile kwararar baki da kuma kula da su yadda ya kamata.
A taron da zai gudana a yau Litinin da gobe Talata a Morocco, ana saran wakilan kasashen duniya za su amince da daftarin, duk da ya ke wasu kasashen Turai da suka fada karkahsin ikon ‘yan ra’ayin rikau irin su Austria da Hungary da Poland na adawa da shirin.
Wasu Magadan Gari da suka halarci taron da ya gudana a Marakesh a karshen mako, kamar na Saliyo Yvonna Aki-Sawyerr da Marvin Rees na Bristol da ke Birtaniya sun bayyana muhimmanci cimma yarjejeniya domin shawo kan matsalolin da ke haifar da kaurar jama’a.