Kimiyya
Wani fasihin matashi a Sokoto ya kir-kiri na’urar Taransfoma
Wani matashi a jihar Sokoto mai suna Anas Aliyu Boyi yace ya shiga harkokin kere – kere ne domin ya taimakawa harkokin fasaha a Najeriya wajen kawo sabbin dabarun fasaha wanda hakan yasa ya kirkiri na’urar Transformer mai caji.
Anas Boyi yace wannan na’ura ta transformer daya kirkira ya kawo sabbin dabaru a cikin ta ba kamar yadda sauran na’urar suke ba kasancewar ita na’urar ana yimata caji ne wadda kuma zaka iya amfani da ita kayiwa wayarka caji da sauran abubuwa.
Boyi ya kara da cewa na’urar ba iya nan ta tsaya ba don kuwa idan kayi mata caji kana iya amfani da ita wajen jona kwayayen hasken wutar lantarki dama fanka kuma ka cigaba da amfani da ita cikin a wannin da suka dara goma.
Anas Aliyu yayi kira ga gwamnati da su rika daukar nauyin irin wadannan matasa domin bunkasa harkokin fasahar su musamman wajen samar musu da kayan da zasu rika cigaba da ayyukan su na kir-kire kir-kire domin bai kamata a rika barinsu haka ba.
An samar da kwalejin kirkire-kirkire da fasaha don bunkasa fasaha – Darakta
Amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen magance matsalar tsaro -Dakta Sani Lawan Malumfashi
Yace kasashen da suka cigaba a fadin duniya sun baiwa bangaren ilimin kimiyya da fasaha muhimmanci wanda hakan yasa kasashen da suka cigaba basa yawan dogaro da irin kayayyakin da ake shigo musu dashi daga wasu kasashe.
You must be logged in to post a comment Login