Connect with us

Labarai

Wani gini mai hawa uku ya ruso a Legas

Published

on

Rugujewar wani gini mai hawa Uku a jihar Lagos ya yi sanadiyyar mutuwar wani kankanin yaro tare da jikkata wasu mutane 6 a yankin Lagos Island.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya fau ne da asubahin yau, lokacin da mutan gidan ke barci.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos Olufemi Oke-Osanyintolu, y ace tuni aka mika gawar yaron zuwa dakin adana gawa yayin da wadanda suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti don fara karbar magani.

Olufemi ya ce da misalin karfe 4 na asubahin Yau Asabar ne suka sami kira daga yankin Freeman cewa wani gini mai hawa uku ya ruguje, inda nan take suka garzaya gurin tare da fara aikin ceto mutanen da ginin ya danne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!