Kimiyya
Wani kamfani ya fara horar da almajirai dabarun kasuwanci ta kafar intanet
Shugaban Kamfanin Aminu Bizi ne ya bayyana hakan yayin da kamfanin kewa almajiran bita kan yadda za su fara gudanar da sana’oin da suka koya na budewa mutane asusun ajiya a bankuna da suran ayyukan sana’a da ake yi a na’urar Computer.
Ya kuma ce zuwa yanzu almajiran da suka koyar da su aikin buɗe asusun ajiya a bankuna da suka fito daga tsangayu daban-daban a kananan hukumomin 8 dake cikin ƙwaryar birnin Kano sun fara cin gajiyar shirin.
Aminu Bizi ya ce yanzu haka sun dauko almajirai biyu a kowacce ƙaramar hukuma dake wajen birnin Kano domin koya musu sana’oin bude asusun banki.
Wasu daga cikin almajiran da suka amfana da tsarin koyar da su sana’oin sun nuna farin cikin su bisa wannan horo da ake musu
Shugaban kamfanin Aminu Bizi ya ce yanzu haka sun fara tattaunawa da gwamnatin jihar Kano kan yadda za su hada hannu wajen taimakawa almajirai da sana’oin da za su dogara da kan su musamman a kokarin da gwamnatin keyi na kawar da barace-barace a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login