Kiwon Lafiya
Wani malami a Jami’ar Ahmadu Bello ya kirkiro wasu nau’ikan maganin zazzabin cizon sauro
Wani malami daga tsangayar kimiyyar harhada magunguna ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria Farfesa Umar Katsayel, ya kirkiro wasu nau’ikan maganin zazzabin cizon sauro wato Malaria guda biyu.
Farfesa Umar Katsayal ya sanar da hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a garin Sandamu kusa da Daura a Jihar Katsina, inda ya ce magungunan za su goga da wadanda ake da su a yanzu wajen yaki da zazzabin na Malaria.
Ya bayyana cewa bayan dogon nazari da bincike-bincike ne ya samar da magungunan, ta hanyar sarrafa wasu saiwowin tsirrai da bawon wasu bishiyo da ake da su a wannan yanki na Sandamu da ke Jihar ta Katsina.
Sannan ya bukaci takwarorinsa masana da kuma kwararru su jajirce wajen fadada tunaninsu da kuma bincike don ganin an kyautata rayuwar al’umma tare da bunkasa tattalin arzikin kasa.
Farfesa Umar Katsayal dai tsohon ‘dan-majalisar wakilai ne da ya taba wakiltar mazabar Sandamu da Mai’aduwa da kuma Daura.