Labarai
Wani tsagi a majalisar Malaman Kano sun sanar da tsige Malam Ibrahim Khalil
Wani tsagi na majalisar malaman Kano sun sanar da tsige shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil.
Malaman sun sanar da ɗaukar matakin ne yayin wani taron manema labarai da suka kira a shalkwatar ƙungiyar ƴan jarida da ke Kano.
Imam Jamilu Abubakar shi ne ya sanar da hakan amadadin malamai daga ƙananan hukumomin 44 na Kano.
Ga jerin dalilin da ya bayyana na ɗaukar wannan mataki.
Takardar:
Assalamu alaikum, sakamakon tattaunawar da Malaman addinin musulunci na jihar Kano daga ɓangarori daban-daban suka yi, wanda suka wakilci ɓangarorin da muke da su wannan jiha mai albarka, a kan damuwar da su ke da ita dangane da yadda ake samun ci baya a majalisar malamai ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Khalil, malamin sun koka da yadda shugaban ya ke gudanar da harkokin majalisar, ga ƙorafe-ƙorafe kamar haka: –
1. Dulmiyar da majalisar cikin siyasa sakamakon yadda shugabanta ya ke fada da dukkan gwamnatin da ta zo, yayi faɗa da Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, yayi fada da Gwamnatin Mai Girma tsohon Gwamna Kwankwaso, ga shi a halin yanzu yana fada da wannan gwamnati ta Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam, dalilin faɗan kuma duka shi ne domin sun hana shi takara, wanda hakan zai iya faruwa rashin cin moriyar gwamnati ga wannan majalisa, kamar yadda ita ma gwamnati ba ta amfana daga shawarwarin wannan majalisa.
2. Rashin faɗaɗa majalisar domin samar da mambobi daga kowacce karamar hukuma a fadin jiha.
3. Rashin yin adalci ga ɓangarorin fahimta da muke da su a wannan jiha, wannan ta sa ba wakilci daga kowanne bangare na Darikar Tijjaniyya, Darikar Qadiriyyah, da kuma kungiyar IZALA da sauran malamai da ba su da alaƙa da bayanin da aka ambata.
4. Sauran mambobin da yake amfani da su, suna kuka a kan sanin rashin sanin me ya ke yi gudana a cikin wannan majalisa.
5. Gabatar da tarurrukan siyasa na kashin kansa a ofis na majalisar malamao.
6. Majalisar ba ta da wani takamaiman aiki da ta ke motsi ko gudanar da wani aiki, majalisar ba ta yin aikinta na samar da fatawa a kan wasu sabbin matsaloli na zamani da su kan zo da kuma sabbin al’amura.
7. Majalisar ta sauka daga kan doran abin da aka gina ta a kai, babu tsarin gudanarwa ko kayan aiki.
8. Irin wannan majalisa ba ta neman dan siyasa mai neman tsayawa takara.
Don haka wannnan majalisa ya kamata ta samu canji wanda ya dace.
Saboda haka wannan gamayyar gamayyar malamai ta rushe wannan tsarin shugabanci na Malam Ibrahim Khalil kuma ta ke ta yi mubaya’a ga Farfesa Abdullahi Sale Pakistan, wannan canji shugaba kadai ya shafa, sauran mataimaka na wannan majalisa suna nan daram.
Allah ya yi mana jagora.
Amadadin gamayyar Malaman Kano Usataz Saifullahi Adam ASSUDANI
Shaikh Halifa Gama
Sheikh Abdul Qadir Ramadhan
Imam Jamilu Abubakar
You must be logged in to post a comment Login