Labarai
Wasu gwamnonin jam’iyyun adawa na dab da komawa APC- Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya tabbatarwa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu cewa wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa na dab da komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Akpabio ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ya yi da Shugaban Ƙasa a fadar gwamnati dake Abuja, inda ya ce nan ba da jimawa ba za su karbi wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa APC.
Haka kuma, ya kara da cewa hakan zai ƙara ƙarfafa jam’iyyar mai mulki, tare da bai wa Shugaban Ƙasa damar aiwatar da manufofin da suka shafi cigaban ƙasar nan cikin sauƙi.
You must be logged in to post a comment Login