Labarai
Wasu jihohi sun ki ba da filayen kiwo ga makiyaya
Wasu jihohin kasar nan guda shida sun ki amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na ware filaye a jihohinsu don samar da wuraren kiwo na zamani ga makiyaya.
Jihohin sun hada da: Delta da Cross River da Anambra da Akwa Ibom da Oyo da kuma Edo.
Tun farko dai wasu jihohi goma sha bakwai na arewacin kasar nan da kuma wasu uku daga kudu da suka hada da: Ekiti da Ondo da kuma Ebonyi har ma da birnin tarayya Abuja sun amince za su ba da filayen ta cikin shirin samar da wuraren kiwo na zamani ga makiyaya.
A watan farbrairun da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta fitar da taswirar wasu muhimman wurare talatin a fadin kasar nan baki daya don samar da wuraren kiwo ga Fulani makiyaya.
A cewar gwamnati, samar da filayen kiwon ga makiyaya zai taimaka gaya wajen kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
A jiya asabar ne jihohin su ka bayyana matsayinsu kan wannan batu, suna masu cewa ba za su ba da ko da takun sawu daya a jihohinsu ba don samar da wuraren kiwo ga makiyayan.
You must be logged in to post a comment Login