Labarai
Wasu kungiyoyi a Kano sun bayyana kokwantonsu kan na’urar BVAS
Bayan da hukumar zaɓe ta Najeriya INEC ta yi gwajin na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS tu ni ƙungiyoyin suka soma nuna fargaba kan yiwuwar sake komawa gidan jiya.
Babban Daraktan ƙungiyar SEDSAC mai rajin tabbatar da Dimokuraɗiyya a Kano Comrade Hamisu Umar Ƙofar Na’isa ya ce, ‘abin da ya banbanta VBAS da Card reader da aka yi amfani da shi a baya shi ne aike wa da sakamako’.
Wannan dai ya biyo bayan bibiyar gwajin da ƙungiyar ta SEDSAC ta yi, kan hakan ne take ganin akwai yiwuwar a iya samun tangarɗar hanyoyin sadarwa kamar yadda aka samu a zaɓen da ya gabata.
Hukumar zaɓe dai ta bada tabbacin cewa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba a samu matsala wajen amfani da na’urar ta VBAS ba a zaɓen da ke tafe
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login