Labarai
Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam
Wani masani kuma mai bincike a fannin magungunan kwari da ke sashin nazarin tsirrai a jami’ar Bayero da ka nan Kano ya bayyana magungunan kwari da manoma ke amfani da su da cewa na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da illa ga lafiyar jikin dana dam.
Alhaji Murtala Ya’u ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na tashar freedom Radio a safiyar yau.
Ya kara da cewa daga cikin illolin da magungunan ke haifarwa akwai cutar ciwon koda ciwon Hanta,wanda suna daya daga cikin cutukan da mutane ke fama da su a yanzu.
A nasa bangaren sarkin Noma na jihar Kano Alhaji Yusuf Na-Dabo yace rashin kula da yadda za’ayi amfani da magugunan na daya daga abinda yake kawo gurbacewar kayayyakin noma.
Bakin biyu sun bukaci manoma da su rinka baiwa gona hutu na dan lokacin wanda hakan yana taimakawa wajen samun kyakyawan amfani gona