Labaran Kano
Wasu tattaba-kunne Sun bukaci gadonsu bayan shekaru 150
Wasu tattataba kunne anan Kano, sun kai kara gaban wata kotun majistiri dake Dorayi domin fitar musu da hakkin su akan wani fili da Baban kakan su marigayi Alhaji Garba ya bayar a wani lokaci can baya domin gina makabarta.
Wannan lamari ya faru ne a unguwar Dorayi dake Karamar Hukumar Gwale a lokacin da wadannan magada suka fuskanci cewa su ma suna da nasu kason a cikin wannan yanki na makabar ta.
A cewar magadan wasu masu hannu da shuni ne suka nuna halin ko’in -kula akan wannan makabarta da gidajen su ke jikinta.
Mutanen da suka rika cin iyakar makabartar sun hadar da Marigayi Alhaji Uba Safiyanu da Alhaji Sabo Jakada da Alhaji Mamuda.
Sulhu tsakanin al’umma zai rage cunkoso a kotuna
Yau Ganduje da Abba kowa zai san matasayin sa-Kotun daukaka kara
Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyu
Wakilin Freedom Radio, Abubakar sabo, ya tattauna da makwabtan wannan makabarta domin jin ta bakin su akan gaskiyar wannan lamari.
Wani mazaunin Unguwar, Dahiru Isa yace yana daga cikin wadanda suka ga mika takardar sammace daga kotun majistiri zuwa ga Mai Unguwar ta Dorayi da kuma wadanda su kayi jagoranci domin zagaye makabartar.
A cewar kotun Mai Unguwar ya raina kiran da tayi masa duk da cewa lauyan Mai Unguwar ya nuna rashin tabbacin zuwan takardar sammacen zuwa fadar mai unguwar.
Dahiru Isa ya kuma kara da cewa tuni kotu aike da ake zargi da hannu cikin badakalar da suka hadar da Nafi’u, Shafi’u da kuma Mai Unguwa zuwa sashin yaki da daba na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano.
Haka zalika wasu daga cikin ‘ya unguwar suna rokon Alkalin Alkalai dasu sauya wajen gudanar da wannan shari’ar dake gudana a halin yanzu.