Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Wasu tattaba-kunne Sun bukaci gadonsu bayan shekaru 150

Published

on

Wasu tattataba kunne anan Kano, sun kai kara gaban wata kotun majistiri dake Dorayi domin fitar musu da hakkin su akan wani fili da Baban kakan su marigayi Alhaji Garba ya bayar a wani lokaci can baya domin gina  makabarta.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Dorayi dake Karamar Hukumar Gwale a lokacin da wadannan magada suka fuskanci cewa su ma suna da nasu kason a cikin wannan yanki na makabar ta.

A cewar magadan wasu masu hannu da shuni ne suka nuna halin ko’in -kula akan wannan makabarta  da gidajen su ke jikinta.

Mutanen da suka rika cin iyakar makabartar sun hadar da Marigayi Alhaji Uba Safiyanu da Alhaji Sabo Jakada da Alhaji Mamuda.

Sulhu tsakanin al’umma zai rage cunkoso a kotuna

Yau Ganduje da Abba kowa zai san matasayin sa-Kotun daukaka kara

Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyu

Wakilin Freedom Radio, Abubakar  sabo, ya tattauna da makwabtan wannan makabarta  domin jin ta bakin su akan gaskiyar  wannan lamari.

Wani mazaunin Unguwar, Dahiru Isa yace yana daga cikin wadanda suka ga mika takardar  sammace  daga kotun majistiri zuwa ga Mai Unguwar ta Dorayi da kuma wadanda su kayi jagoranci domin zagaye  makabartar.

A cewar kotun Mai Unguwar ya raina kiran da tayi masa  duk da cewa lauyan Mai Unguwar  ya nuna rashin tabbacin  zuwan takardar sammacen zuwa fadar mai unguwar.

Dahiru Isa ya kuma kara da cewa tuni kotu aike da ake zargi da hannu cikin badakalar da suka hadar da Nafi’u, Shafi’u da kuma Mai Unguwa zuwa sashin yaki da daba na rundunar  ‘yan sanda reshen jihar Kano.

Haka zalika wasu daga cikin ‘ya unguwar suna rokon Alkalin Alkalai dasu sauya wajen gudanar da wannan shari’ar dake gudana a halin yanzu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!