Labarai
Wasu Unguwannin Kano sun samu gurbatar Iska- Gwamnatin Kano

Wani rahoto na mako-mako kan yanayin kyawun iskar da mutane ke shaka da gwamnatin Kano ke fitarwa, ya nuna cewa an samu gurɓatar iska a wasu unguwanni a cikin ƙwaryar birni, inda hakan ke ƙara ta’azzara yaɗuwar cutuka a cikin al’umma.
Rahoton, wanda Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta fitar bayan gwajin lafiyar iska da ta yi tsakanin ranakun 26 zuwa 30 ga watan da muka yi bankwana da shi na Mayu, ya nuna cewa unguwanni kamar su Gaida da Ja’en da Sabon Titi da Sharada Kasuwa, ba su da lafiyayyar iska, inda sakamakon ya nuna akwai gurɓatar iska a waɗannan unguwanni.
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Kano na shirin kai ɗauki a wadannan unguwanni sakamakon gurɓacewar iska, inda ta nuna damuwa kan karin gurɓacewar yanayi da ake samu a jihar.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya wallafa rahoton a shafin sa na Facebook.
Ya kuma nuna cewa kula da muhalli hakki ne na gaba dayan al’umma ba wai gwamnati kaɗai ba.
You must be logged in to post a comment Login