Labarai
Wasu ‘yan Mari sun farwa malaman su
Bayan umarni da Gwamnatin jihar Kano tayi akan kulle dukkan gidajen Marin da yake fadin jihar Kano hakan ya jawo ce-ce-ku-ce da kuma kace-nace tsakanin al’ummar jihar nan, ganin cewa hakan bazai kawo mafita ba ga al’umar jihar Kano.
Ana cikin haka ne sai kwatsam aka samu labarin cewa wasu daga cikin ‘Yan Marin da aka sako bayan umarnin da gwamnati ta bayar sai suka koma tsohuwar Makarantar ta su ta Mari domin daukar fansa akan Malaman na su.
Malaman makarantar “Yan Marin ta Malam Hashimu mai Dan Mari dake Sabuwar Gandu sun koka kan barazana iri daban – daban da suke fuskanta musanman daga bangaren yaran da aka sako domin kuwa sun dawo musu dauke da makamai da sunan daukar fansa.
Daya daga cikin Malaman ‘Yan Marin mai suna Abubakar Hashim ya bayyana wa manema labarai cewa sun zo neman sa a lokacin da baya nan sai suka bar sakon cewa a fada mishi in suka ganshi sai sun yanka shi.
Dole ne na maida da na makarantar ‘Yan Mari-Mahaifi
Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari
‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano
Ko da Freedom Radio ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewar, ‘yan sanda sun samu nasarar kama wasu daga cikin ‘Yan Marin yayin da suka musanta batun duk kuwa da cewa an kama su da makamai, suna masu cewar su zuwa suka yi su gaida Malaman.
Tuni da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano CP Ahmed Iliyasu ya umarci da akai ‘Yan Marin sashin bincike da yake shalkwatar rundunar ‘yan sanda a Bompai don gudanar da bincike kan musababin lamarin don tabbatar da adalci.
A gefe guda kuma an samu wasu ‘Yan marin wanda su kuma sukace su sun sami damar guduwa ne daga gidan tun kafin ma a sake su inda suka fita da Marin a kafar su sukaje wajen masu kira suka cire musu kuma suka siyar dashi suka karbi kudin.
A cewar su irin horon da ake bayarwa a gidan Marin ya wuce gona-da-iri, hasali ma sai Malaman sun sha kwaya sannan suke yi musu horo.